Monday, May 12
Shadow

An kàshè shanu 37 a jihar Plateau

Akalla shanu 37 aka harbe a ƙauyen Tashek da ke ƙaramar hukumar Riyom ta jihar Plateau a jiya Lahadi.

A cewar shugaban reshen jihar na kungiyar Miyetti Allah , Ibrahim Yusuf Babayo, lamarin ya faru ne kusan ƙarfe 1:00 na rana.

Wannan harin na baya-bayan nan ya faru ne kasa da mako guda bayan wani hari makamancin haka a ƙauyen Tanjol, wanda ma yana cikin ƙaramar hukumar Riyom, inda ‘yan bindiga suka budewa makiyaya wuta, suka jikkata makiyaya biyu tare da kashe shanu biyar.

Shugaban kungiyar ya bayyana harin a matsayin wanda ba tare da wani dalili ba, yana mai cewa lamarin wani ƙulli ne na masu aikata hakan domin cimma wani ɓoyayyen buri.

Karanta Wannan  Kasar Nijar ta koro karin 'yan Najeriya 392 zuwa gida

Babayo ya ce, “’Yan bindiga sun mamaye yankin suka fara harbin shanun da ke kiwo, wanda ya kai ga mutuwar shanu 37 da kuma raunata wani makiyayi. Da zarar bayan harin, na kira kwamandan sashen Operation Safe Haven da ke Riyom domin sanar da shi, kuma daga baya ya tura dakarunsa zuwa wurin domin tantance halin da ake ciki.”

Da aka tuntubi shugaban matasa a ƙaramar hukumar Riyom, Song Bitrus, ya ce, “Ban san da wannan lamarin ba. Sai dai daga gare ka nake ji yanzu. Ban sani ba.”

Mai magana da yawun Operation Safe Haven, wata rundunar tsaro da ke kula da zaman lafiya a jihar, Manjo Samson Zhakom, bai amsa saƙon da aka aika masa ba har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoto.

Karanta Wannan  Matar soja Abbas mai suna Husaina Iliyasu ta cika gwarzuwa kuma jarumar da samun irin ta sai an tara mata 1000

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *