Gwamnatin Najeriya ta ce an kusa fara biyan masu yi wa ƙasar hidima alawus na naira 77,000 da aka amince za a riƙa biyansu na wata-wata.
Darakta-janar na NYSC, Birgediya Janar YD Ahmed ya bayyana haka a ranar Talata a wata sanarwa da kakakin NYSC, Caroline Embu ta fitar kamar yadda tashar Channels ta ruwaito.
Ahmed ya ce zai mayar da hankali kan jin daɗin masu yi wa ƙasa hidima, inda ya ƙara da cewa tuni shirye-shirye sun kammala domin fara biyan sabon alawus ɗin.
An dai ƙara alawus ɗin ne tun bayan da gwamnatin Najeriya ta ƙara mafi ƙarancin albashin ma’aikata a ƙasar.