Thursday, April 17
Shadow

An min Wahayi, Allah ya gayamin kada in sake in aske gashin kaina>>Inji Fasto Jimmy Odukoya bayan da ake ta kiraye-kirayen ya aske kitson da yayi a kansa

Fasto Jimmy Odukoya na cocin Fountain of Life church ya bayyana cewa, An masa wahayi inda Allah ya gaya masa kada ya sake ya aske gashin kansa.

Faston ya bayyana wa mabiyansa hakane a gaban mabiyansa yayin da yake musu wa’azu.

Yace kanwarsa ta bashi shawarar aske gashin kansa musamman saboda kada mutane su rika masa wani irin kallo.

Saidai yace bai yanke shawara ba sai da ya nemi taimakon Allah kuma an masa wahayi inda aka ce kada ya aske gashin kan.

Yace ya tura kanwar tasa ma yace ta je ta yi addu’a akai inda ta dawo tace itama an mata wahayi cewa kada ya aske gashin kan nasa.

Karanta Wannan  Magidanci ya kkashe diyarsa me shekaru 15 saboda yin TikTok

Inda ya bata amsar cewa shima dama an gaya masa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *