An saka wasu kalamai da ake amfani dasu a Najeriya a cikin Dictionary din turanci na kasar Ingila.
Kalam da aka saka yawanci na Turancin Pidgin ne wanda aka fi sani da Broken English.
Kalaman sune “Japa” wadda ke nufin tserewa daga Najeriya zuwa turai dan cirani, sai kuma kalmar “Agbero” wadda ke nufin dan tasha ko kuma marasa jin magana na kan titi, Akwai kuma kalmar “419” dake nufin rashawa da cin hanci ko zamba cikin aminci.
Sauran kalmomin sun hada da cross-carpet, cross-carpeting, eba, Edo, gele, Kanuri, Kobo, Naija, suya(watau tsire), Yahoo, Yahoo boy and Yarn Dust.
Jami’in tuntuba wanda dan Najeriya ne a Oxford English Dictionary, Kingsley Ugwuanyi ne ya tabbatar da hakan.