
Ministan tsaron Najeriya, Mohamamd Badaru Abubakar ya ce sauya dabarun tsaro ne abun da ya kamata a mayar da hankali ba wai taro kan tsaro ba, da majalsair dattawwan ƙasar ta nemi a yi ba.
Haka kuma ya musanta zargin da majalisar wakilan ƙasar ta yi na cewar ƴan bindigar na amfani da makaman da suka fi na jam’an tsaron ƙasar.
A ranar Talata ne dai majalisar dattawan Najeriya suka buƙaci da a shirya wani taro kan harkokin tsaro, don samar da hanyoyin magance matsalar.
Sai dai a yayin ganawa da manema labarai na ministoci da ya gudana a jihar Laraba ministan tsaron na Najeriya Mohammad Badaru Abubakar ya ce sakae dabarun yaƙi da mastaalr tsaro ya kamata a yi ba wai taro ba a halin da ake ciki a ƙasar.
“Idan ka yi taron ƙasa kan tsaro, mutane za su zo, su fadi abin da suke so, mu kuma za mu ɗauka, sannan sai mu koma, don sake sabunta tsarin mu na tsaro, sannan sai babban hafsan tsaron ƙasa shi ma ya bayar da umarni bisa dabaru da tsarin da aka bayar. Abun da majalisar suke ƙoƙarin yi, shi ne, su tara mutane su tattauna kan batutuwa. Za ka ji maganganu iri-iri.” in ji Badaru.