An sanar da ranar da za a binne Fafaroma.

Fadar Vatican ta tabbatar da cewa za a yi jana’izar marigayi, Fafaroma Francis da ƙarfe 8 na safe agogon GMT, a ranar Asabar mai zuwa.
Hakan na zuwa ne yayin da fadar ta fitar da bidiyon da ke nuna mamacin kwance a cikin akwatin gawa, a cocin Casa Santa Marta da ke gidansa.
Bidiyon ya nuna gawar Fafaroma sanye da jar doguwar riga da hularsa ta fafaroma da kuma carbi a hannunsa.
A ranar Laraba ne za a mayar da gawar St Peter’s Basilica, inda za a ajiye shi domin mutane su yi masa bankwana har zuwa ranar Asabar da za a binne shi.
Fafaroma Francis ya mutu ne a ranar Litinin yana da shekaru 88 a duniya, sakamakon bugun zuciya.