Thursday, May 22
Shadow

An Tura Shi Gaidan Yari Saboda Ya Yada Labarin Cewa Gwamnan Kebbi Zai Bar APC

An Tura Shi Gaidan Yari Saboda Ya Yada Labarin Cewa Gwamnan Kebbi Zai Bar APC.

Muna rokon gwamnatin jihar Kebbi da ta dubi girman Allah ta saki wannan bawan Allah Muktar da aka kama a yau aka tura gidan yari.

Laifin Muktar daya ne, saboda ya yi ‘sharing’ wani ‘posting’ wanda wata gidan jarida ta ruwaito na cewa ” Gwamnan jihar Kebbi zai bar jam’iyyar APC”.

Sanadiyyar wannan posting din da wannan bawan Allah ya yi sharing a page dinsa, yau an kama shi an gurfanar da shi kotu. Babu wani jayayya aka wuce da shi gidan yari.

Muktar ya fito ya bada hankuri na wannan posting din da ya yi, amma kuma ba’a duba masa ba, saida aka kama shi aka gurfanar da shi a kotu.

Karanta Wannan  IKON ALLAH: Ya Yi Gaŕķuwa Da Yaro Dan Shekara Bìýu, Inda Ya Nemi A Ba Shi Naira Milyan Hamsin Kùďin Fansa

Mun san Gwamnan jihar Kebbi mai adalci ne, dan Allah ka dubawa wannan bawan Allah. Yana da iyali kuma yana da ‘yan uwa.

Daga Murjanatu Diri

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *