Monday, March 24
Shadow

An yi gàrkùwà da soja da wasu sauran mutane a Abuja

Rahotanni daga babban birnin tarayya, Abuja na cewa an yi garkuwa da wata sojar ruwa dake aiki a hedikwatar tsaro ta kasa tare da wasu mutane.

Lamarin ya farune a Mpape dake Abuja ranar Juma’a inda aka shiga har gida aka tafi da wadanda aka yi garkuwar dasu.

Wata majiya ta shaida cewa, wadanda aka yi garkuwa dasu din an kira iyalansu inda ake neman Naira Miliyan 100 a matsayin kudin Fansa.

Jimullar mutane 3 ne aka yi garkuwar dasu, ciki hadda sojar me suna Lt. Cynthia Akor.

Hukumomin soja dai basu ce uffan kan lamarin ba.

Karanta Wannan  Sowore ya baiwa 'yan Najeriya shawarar su je su shiga gidaje 753 na Abuja da gwamnati ta kwace saboda nasu ne

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *