Friday, December 5
Shadow

An zane wasu masoya bisa saduwa kafin aure a Indonesiya

An zane wasu masoya bisa saduwa kafin aure a Indonesiya.

An yi wa wani mutum da wata mata bulala ɗari-ɗari kowanne a bainar jama’a a lardin Aceh mai a kasar Indonesia a yau Laraba bayan da wata kotun shari’ar Musulunci ta same su da laifin yin jima’i kafin aure.

An haramta yin jima’i tsakanin masoya da basu yi aure ba a garin na Aceh, wanda ya kafa tsarin shari’ar Musulunci.

Indonesiya ta haramta yin jima’i ba tare da aure ba a sabon kundin dokokin Shari’ah a 2022 amma dokar ba za ta fara aiki ba sai shekara mai zuwa.

Sai dai kuma an yi wa mutanen biyu bulala ɗari-ɗari ta hanyar yin goma-goma a yayin da wasu tsirarun jama’a ke kallo a wani wuri da ke Aceh babban birnin lardin, inda mace ce ta yi wa matar da ake zargin bulala, a cewar wani wakilin AFP da ke wajen da aka yi hukuncin.

Karanta Wannan  Kasar Ìran ta yiwa kasar Israyla mummunan kutse inda ta kwashi bayananta game da makamin kare danginta

Hakazalika an yi wa wasu mutane uku bulala 49 dukkanin su bisa zargin su da yin caca da shan barasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *