
Masu sharhi a kafafen yada labarai da kafafen sada zumunta musamman daga kudancin Najeriya kuma mafi yawanci Kiristoci na ci gaba da yin Allah wadai da hutun da wasu jihohin Arewa suka bayar a makarantu saboda zuwan watan ramadana.
Ko da a jiya, saida kungiyar Kiristocin CAN ta fitar da sanarwar cewa, bata goyon bayan bayar da wannan hutu i da tace babban abin takaici ma shine ba’a tuntubeta ba kamin bayar da wannan hutu.
Jihohin da suka bayar da irin wannan hutu sun hada da Katsina, Kano, Kebbi da Bauchi.
A maganar da Kungiyar kiristoci ta CAN tayi tace akwai kasashen da suka fi ‘yan Najeriya yawan musulmai amma duk da haka basu bayar da hutun Azumin watan Ramadana a makarantun su ba maimakon hakan sun rage yawan awannin da ake zuwa makarantunne.
Da safiyar yau, Litinin ma Kafar Hutudole ta yi karo da wani sabon rubutu da aka wallafa akan maganar bayar da hutun makarantun na Azumun watan Ramada wanda ake cewa bai dace ba a gidan jaridar Daily Trust.
Tun ranar 1 ga watan Ramadana kafar hutudole ta kawo muku rahoto da sharhi akan yanda muka lura wasu daga kudancin kasarnan musamman Kiristoci ke dariya da ba’a da zunde game da hutun da aka bayar a makarantun Arewa saboda zuwan watan Ramadan duk da wasu sun karyata wannan rahoton namu.