
Rahotanni sun nuna cewa canja sunan jami’ar UNIMAID dake Maiduguri zuwa sunan Muhammadu Buhari University baiwa wasu dadi ba.
Cikin wadanda suka nuna rashin jin dadin wannan canjin suna akwai tsaffin daliban makarantar, da wasu daliban makarantar na yanzu, da kuma wasu sauran ‘yan kasa.
Tuni an fara kiran shugaba Tinubu ya yanje wannan canjin suna.
A wata budaddiyar wasika da aka aikewa shugaba Tinubu wadda Opeyemi Olatinwo ya rubuta, tace maganar gaskiya canja sunan zai sa jami’ar UNIMAID ta rasa tarihinta da kwarjininta.
Shugaba Tinubu ya sanya sunan Buhari a jami’ar ne dan a rika tunawa dashi.