
Ana yada rade-radin cewa Arzikin Atiku Abubakar ya ja baya ba irin na da ba, dan ba lallai ma yana da kudin da zai iya zagaya Najeriya yayi yakin nema zabeba a shekarar 2027.
Duk da yake cewa wannan hasashe ne na masu lura da al’amuran yau da kullum na siyasar Najeriya, ba abin mamaki bane idan ya kasance Gaskiya.
Dalili kuwa shine Atiku Abubakar sau 6 yana fitowa yakin neman zaben Najeriya amma bai yi nasara ba, sannan kudaden da yake kashewa wajan yakin neman zaben Biliyoyin Naira ne musamman idan aka lura da jirage da motoci da ake tafiya dasu zuwa jihohin Najeriya 36 da Abuja dan yakin neman zabe, duk a Aljihunsa ne.
Ga kudin man motocin ga kudin sallamar da za’a ba ma’aikata ga kudaden da zai bayar duk gurin wani basaraken da yaje neman goyon bayansa da sauransu.
Lallai ida an ce Atiku yanzu bashi da kudin da zai yi yakin neman zabe ba abin mamaki ba ne, dan kuwa ba kowa zai iya abinda yayi ba.