
Tsohon ɗan takarar kujerar sanatan Kano ta Tsakiya, Alhaji Abdulsalam Abdulkarim Zaura ya ce za su yi duk mai yiwuwa domin ganin sun sulhunta tsakanin jagororin siyasar jihar: Rabiu Musa Kwankwaso da Abdullahi Umar Ganduje da Ibrahim Shekarau.
Zaura ya ce haɗin kan manyan jagororin zai taimaka wajen gyara siyasar jihar, tare da samar da cigaba ta yadda jihar za ta yi gogayya da jihar Legas da wasu jihohin da suka ci gaba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Zaura ya ce, “irin adawar siyasa da ake yi a Kano ba ta da amfani. A shirye nake in shige gaba wajen samar da maslaha tsakanin Kwankwaso da Ganduje da Shekarau. Ya kamata mu fifita ci gaban Kano sama da son ranmu. Da zarar an samu wannan nasarar, Legas da sauran jihohi sai sun yi koyi da Kano wajen siyasa ta hankali da ci gaba.”
A baya Abdulmumin Jibrin Kofa da Murtala Sule Garo da Baffa Babba Danagundi duk sun bayyana irin buƙatar a lokuta daban-daban.