Friday, December 5
Shadow

Ana ta caccakar wani ɗansanda saboda ya ɗaura wa Ganduje takalmi

Ana ta caccakar wani ɗansanda saboda ya ɗaura wa Ganduje takalmi.

Wani ɗansanda na shan matsin lamba a kafafen sada zumunta bayan da aka gan shi ya na ɗaura wa Abdullahi Umar Ganduje, shugaban jam’iyyar APC mai mulki, igiyar takalmi.

A cikin wani bidiyo da ya karade intanet, an ga Ganduje tsaye yayin da dansandan da ba a bayyana sunansa ba ya durƙusa ya na ɗaura masa igiyar takalmi.

Bidiyon da ya bayyana a yanar gizo ranar Litinin ya janyo ce-ce-ku-ce daga jama’a.

Wasu sun yi mamakin yadda dan sanda da ke cikin kayan aiki zai aikata irin wannan abu, yayin da wasu kuma suka ce wata kila Ganduje ya taka muhimmiyar rawa a rayuwar dan sandan.

Karanta Wannan  Kai Duniya: Ji yanda Wani Marar Imani ya tsallaka Maqabara ya Qàqùlò Qàbàrìn Jariri a Potiskum, Jihar Yobe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *