
Wani mutum da yayi ikirarin ya mutu a yayin da ake tsaka da yi masa tiyata ya bayyana cewa ya hadu da Annabi Isa(AS) watau Jesus kuma wai har ya nuna masa Aljannah.
Mutumin me suna Mike McKinsey dake California ta kasar Amurka ya bayyana cewa, yayi mutuwar ne ta mintuna 45.
Likitoci sun bayyana cewa aikinsa ne mafi mamaki da hadari da suka taba yi inda suka ce wai ya mutu na dan wani lokaci a yayin da suke masa aikin cire appendix.
Sun ce zuciyar mutumin ta daina bugawa sannan ya daina numfashi amma sun yi nasarar dawo dashi.
Yace da ya mutun, ya ga Jesus wanda yayi kama da Balarabe.
Yace Jesus din ya bashi hannu ya daukeshi zuwa wani guri me kyau da bai taba gani ba.
Yace anan ne yasan cewa ba zai mutu ba.
Ya kara da cewa, sai kawai ya farfado inda ya tabbatar cewa lallai mutuwa yayi ya dawo.
Saidai yace shi kam baya tsoron mutuwa.