
Rahotanni na ta yawo musamman a kafafen sada zumunta inda ake zargin cewa, Kasar Amurka na da hannu a mutuwar fafaroma.
Hakan ya farune bayan da Fafaroma ya mutu, awanni kadan bayan ganawar da yayi da mataimakin shugaban kasar Amurka, J.D. Vance.
Saidai me yasa wasu ke zargin Amurkar da hannu a kashe Fafaroma?
Fafaroma dai na daya daga cikin mutanen dake adawa da kisan Falasdinawa musamman fararen hula da suka hada da kananan yara da mata da Kasar Israela ke yi.
Hakanan Fafaroma na kiran a kare hakkin ‘yan Luwadi da Madigo, duk da yake da yawa daga cikin fastoci basa tare dashi akan hakan.
Hakanan bayan da J.D. Vance yaje fadar Fafaroman, Fafaroman yaki ganawa dashi a hukumance.
Saida aka kammala taro a hukumance sannan J.D. Vance ya je ya gana da Fafaroma.
Saidai a sakonsa na Ta’aziyya, J.D Vance yace a lokacin da ya hadu da Fafaroma akwai alamun rashin lafiya tare dashi sosai.
Babu dai wata hujja ta zahiri data tabbatar da wannan zargi da akewa kasar Amurka.