
Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnatin tarayya ta cire sunan shugabar bankin Fidelity Dr. Nneka C. Onyeali-Ikpe daga sunayen mutanen da take bincika.
Babban Lauyan Najeriya, kuma Ministan shari’a, Lateef Fagbemi (SAN) ne ya fara bincikenta a baya bisa zargin damfara da Almundahana.
Wasu daga cikin zarge-zargen da ake mata shine amfani da kudin bankin wajan sayen hannun Jari na miliyoyin Naira.
Saidai gashi yanzu da Alama Gwamnatin ta yafe mata.