
Ma’aikata a tashar Nukiliya ta kasar Ingila me suna Hinkley Point C sun koka da barkewar Annobar beraye.
Berayen na kawo tarnaki a ayyukan tashar makamashin inda suke neman a kai musu dauki.
Wasu ma’aikatan tashar da aka zanta dasu sun ce berayen sun yi yawa inda suka ce abinda ke kawo su hadda rashin kulawa da tsaftar tashar.