Friday, December 5
Shadow

APC ta lashe zaɓen ƙananan hukumomi 20 cikin 23 na Rivers

Jam’iyyar APC ta lashe ƙananan hukumomi 20 cikin 23 a zaɓen ƙananan hukumomi jihar Rivers da aka gudanar a jiya Asabar.

A ɗaya ɓangaren kuma, jam’iyyar PDP mai mulki a jihar, ta samu nasarar lashe ƙananan hukumomi uku, kamar yadda hukumar zaɓen jihar ta sanar.

Dakataccen gwamnan jihar, Siminalayi Fubara ya sha kaye a ƙaramar hukumarsa ta Opobo-Nkoro, inda ɗan takarar jam’iyyar APC ya lashe zaɓen.

Shugaban hukumar zaɓen, Dr Michael Odey ne ya sanar da sakamakon zaɓen a hedkwatar hukumar da ke titin Aba a Fatakwal kamar yadda jaridar Punch mai zaman kanta ta ruwaito.

A bara dai an yi wani zaɓen, inda Fubara ya tsayar da na hannun damarsa a jam’iyyar APP, inda suka doke ƴan takarar Wike a zaɓen, amma mutanen tsohon gwamnan suka je kotu, inda aka yi ta tafka shari’a har kotun ƙoli ta soke zaɓen daga baya.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: A baibul an gaya mana cewa dolene Miji ya tabbatar yana biyawa matarsa bukatar Jìmà'ì, idan ba haka ba, zata iya cin amanarsa>>Inji Wannan Matar

Bayan sulhu tsakanin Fubara da Wike wanda Tinubu ya jagoranta aka shirya wannan zaɓen, inda tun farko aka ce an tsara yadda ake so ta kasance.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *