Friday, December 5
Shadow

APC ta zargi Gwamnatin Kano da ciyo bashin Dala Miliyan 6.6 daga ƙasar waje tare da neman bahasin yadda aka yi da kuɗaɗen

APC ta zargi Gwamnatin Kano da ciyo bashin Dala Miliyan 6.6 daga ƙasar waje tare da neman bahasin yadda aka yi da kuɗaɗen

Wata ƙungiya a cikin jam’iyyar APC a jihar Kano mai suna APC Patriotic Volunteers ta zargi gwamnatin jihar da karɓar bashi daga ƙasashen waje har Dala Miliyan 6.6 ba tare da bayyana inda kuɗaɗen suka tafi ba.

Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Alhaji Usman Alhaji ne ya yi wannan zargi a taron manema labarai da aka gudanar a Kano a yau Laraba.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa taron manema labaran an shirya shi ne domin nazarin ayyukan gwamnatin jam’iyyar NNPP a Kano cikin shekaru biyun da ta yi a kan mulki.

Karanta Wannan  YANZU-YANZU: Gwamnatin Tinubu ta fara sayar da buhun shinkafa a kan farashin dubu Arba'in N40,000

A cewar Alhaji Usman, ƙungiyar na da hujjoji daga Ofishin Kula da Lamuran Bashi na Ƙasa (DMO) da ke nuna cewa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta karɓi bashin kasashen waje a cikin shekaru biyun da suka gabata.

Ya zargi gwamnatin da cewa duk da karɓar bashin waje, ta sake karɓar kuɗi da dama daga wasu hanyoyi, amma babu wani abin da za a iya gani da ke nuna inda kudaden suka tafi.

Alhaji Usman ya kuma kalubalanci gwamnatin jihar da ta tabbatar da ikirarin gaskiya da bayyana cikakken bayanin bashin da ke kan jihar a halin yanzu.

Ƙungiyar ta kuma zargi gwamnatin Gwamna Abba da almubazzaranci da kuɗin asusun kula da muhallin da gwamnatin tarayya ta fitar, waɗanda suka kai Naira biliyan 5.1.

Karanta Wannan  SERAP ta ɓuƙaci Tinubu ya hana ministan Abuja da gwamnoni bai wa alƙalai motoci da gidaje

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *