
Sakataren jam’iyyar APC reshen kudu maso kudu, Dr Blessing Agbomhere ya aikawa shugaban hukumar yaki da rashawa da cin hanci, EFCC, Ola Olukoyede da wasika cewa Tampolo bai aikata komai ba.
Wata majiya daga EFCC ce ta bayyanawa kafar jaridar Leadership da hakan.
Sakataren APC din yace Tampolo bai aikata komai ba wanda ya sabawa Doka.
Dr. Agbomhere wanda kuma lauyan Tampolo ne yace EFCC ta janye takardar gayyatar da tawa Tampolo.
Duk wannan na faruwane bayan da aka ga Tampolo a wajan wani biki yana wulakanta Naira, abinda hukumar ta EFCC ta hukunta mutane da yawa a Najeriya saboda shi.
Da yawa sun ce indai wannan doka ba ta son kai bace, ya kamata a gayyaci Tampolo, saidai da yawa na ganin hakan ba zai yiyu ba.
Saidai Tuni EFCC ta aikewa da Tampolo takardar gayyata inda tace ya bayyana a gabanta nan da 19 ga watan Mayu a ofishinta dake Abuja.
Saidai lauyan nasa ya nemi EFCC ta janye wannan takardar gayyata.