Sunday, May 25
Shadow

Atiku Da Tinubu bai kamata su fito takarar shugaba cin Najeriya a shekarar 2027 ba>>Inji Baba Ahmad

Tsohon hadimin shugaban kasa, Dr. Hakeem Baba Ahmad ya bayyana cewa, da Atiku Abubakar da Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu bai kamata su tsaya takarar shugabancin Najeriya a shekarar 2027 ba.

Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan Talabijin na ChannelsTV.

Yace maganar tsayawa takarar Atiku a 2027 bai kamata ba, tunda ya gwada bai yi nasara ba, kamata yayi ya koma gefe ya zama mai bayar da shawara.

Yace Tinubu ma haka ya dace dashi musamman ma lura da yanda tattalin arzikin Najeriya ya samu kansa.

Yace har Peter Obi duk kamata yayi su hakura in kuma basu hakura ba, ‘yan Najeriya su musu ritaya.

Karanta Wannan  Shugaba Tinubu ya dawo Abuja

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *