
Tsohuwar tauraruwar BBN, Uriel Oputa ta bayyana cewa, Azumi na kara mata karfin sha’awa.
Ta bayyana hakane a wani rahoto na jaridar Punchng.
Ta hayyana cewa ta fara yin Azumi ne wanda take karyawa da misalin karfe 6 na yamma bayan da ta fara samun matsalar rashin narkewar abinci kuma bata samun shiga bayi yanda ya kamata.
Tace kuma tasan tana cin abinci me gina jiki, dan hakane sai ta yanke shawarar fara Azumin.
Tace data fara azumin ta ji jikinta ya dawo daidai sannan har karfin sha’awarta ya karu sosai.