Friday, December 5
Shadow

Ba a zaɓe mu don mu yi fada da shugaban ƙasa ba – Akpabio

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana cewa ‘yan Majalisar Dokoki ta Kasa ba a zabe su bane domin su yi takaddama da bangaren zartarwa na gwamnati, sai dai don su inganta manufofin da ke kara ci gaban kasa.

Shugaban Majalisar Dattawan ya yi wannan bayani ne a wani taron kaddamar da wani fim da za a saki domin bikin cika shekaru biyu da mulkin Bola Tinubu.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun fadar shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Talata, Akpabio ya jaddada muhimmancin hadin gwiwa tsakanin bangaren majalisa da na zartarwa, inda ya ce: “Lokacin da aka zabe ka zuwa Majalisar Dokoki, ko dai a Majalisar Dattawa ko Wakilai, al’ummarka ba za su ba ka safar dambe ba. Ba gasa ce ta dambe ba. An tura ka ne domin ka yi aiki cikin hadin kai don amfanin Najeriya.”

Karanta Wannan  A rayuwarnan wadanda ka taimaka kawa abin arziki ne ke komawa su zama makiyanka>>El-Rufai ya koka

Shugaban Majalisar Dattawan ya jaddada cewa dangantaka tsakanin bangarorin gwamnati biyu ta kasance cikin kwanciyar hankali a cikin shekaru biyu da suka wuce, saboda hangen nesa na ci gaban kasa.

“Idan ka bata duka karfinka wajen yakar bangaren zartarwa, wa zai yi aikin ci gaban Najeriya?” in ji shi. Ya kara da cewa wannan gwamnatin ta bambanta a tarihin Najeriya, domin shugaban kasa, uwargidansa, da mataimakin shugaban kasa duk tsofaffin ‘yan majalisa ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *