
Gwamnatin jihar Kaduna ta yi karin haske kan rahotannin dake cewa Bam ya fashe a Unguwar Abakpa dake jihar.
A jiya ne dai rahotanni suka rika yawo cewa Bam din ya fashe ne inda har ya kashe yara biyu da jikkata wasu mutane 3, Kamar yanda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Saidai a jawabin da gwamnatin jihar ta fitar ta bakin Kwamishinan tsaron cikin gida, Sir James A. Kanyip, KSM; PhD tace rahoton ba gaskiya bane.
Yace abinda ya faru shine, Bindiga hadin gida ce ta tashi ba tare da shiri ba shine abinda ya faru.
Yace Tuni jami’an tsaro suka kai dauki wajan da abin ya faru sannan ana kan bincike.