
Tsohon shugaban kasa na mulkin Soja, Janar Yakubu Gowon ya bayyana cewa, ba dan kiyayya ga wasu mutanene yasa aka yi yakin basasa ba a Najeriya.
Ya bayyana hakane ranar Asabar a Abuja inda yace dalilai na neman hadin kan kasa ne suka sa dole suka fito aka yi yakin basasa dasu.
Yakubu Gowon ya bayyana muhimmancin yafiya, da sasanci da hadin kai.
Ya bayyana cewa, ya tuna da lokaci mafi wahala a rayuwarsa, watau lokacin yakin basasa, inda yace abu ne da bashi da zabi akansa, kuma yayi abinda ya kamata dan ganin an hada kan kasarnan.
Janar Yakubu Gowon dan shekaru 91 yace shima yayi asara a yakin basasa dan kuwa a yakin basasa ne ya rasa babban abokinsa, Major Arthur Unegbe.