Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad ya karyata ikirarin Bankin Duniya na cewa, Tsare-tsaren gwamnatin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu suna aiki.
Wakilin Bankin Duniya, Dr Ndiame Diop A baya a wajan wani taro a Abuja ya bayyana cewa, suna sane da ‘yan Najeriya na cikin wahala amma tsare-tsaren da gwamnati ta dauko masu kyau ne dan haka a kara hakuri.
Yayi gargadin cewa idan aka dawo da biyan tallafin man fetur da na dala kasar ta Najeriya na iya fadawa cikin balai.
Saidai a martaninsa kan wannan lamari, Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad yace wannan magana ba gaskiya bace, tsare-tsaren na gwamnatin Tinubu basa aiki.
Yace a karin farko da gwamnati ta kawo wadannan tsare-tsare da canje-canje sun goyi bayanta amma maganar gaskiya yanzu mutane suna cikin wani hali.
Yace mutane na fama da talauci da yunwa basa iya biya kudin wutar lantarki da sauransu dan haka yayi kira ga gwamnatin tarayyar da ta sake duba wannan mataki data dauka.
Yace mutane a yanzu suna kule da ‘yan siyasa irinsa sosai.