Ministan kudi Wale Edub ya ce ba maganar komawa baya game da batun cire tallafin man fetur dana Dalar Amurka.
Ya bayyana hakane a yayin da yake karbar sabon karamin ministan kudi,Doris Uzoka Anite a Hedikwatar ma’aikatar dake Abuja ranar Litinin.
Ya bayyana farin ciki da samun karamar Ministar wadda yace zata taimaka wajan cimma tsare-tsaren gwamnatin.
A nata bangaren, Ministar tace zata yi aiki da masu ruwa da tsaki dan tabbatar da ganin ci gaban tattalin arziki.