
Dan majalisar wakilai daga jihar Kaduna wanda da ne a wajan tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, watau Bello El-Rufai ya bayyana cewa, ba ruwansa yayin da aka kirashi ya dauki mataki kan batan dan fafutuka na jihar Jigawa, Abayo Roni.
Bello El-Rufai ya bayyana cewa, matashin ya tsani mahaifinsa kuma ya rika sukar ayyukan da yake yi, yace yana ma kokarin ya kaishi kara.
Yace amma yana fatan yana cikin koshin lafiya.
