
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour Party a zaben shekarar 2023, Peter Obi ya bayyana cewa, shekaru 4 sun isheshi ya gyara Najeriya idan aka zabeshi shugaban kasa.
Peter Obi ya kuma baiwa magoya bayansa tabbacin zai tsaya takarar shugaban kasa a 2027.
Ya bayyana hakane a ganawar da yayi da manema labarai a Abuja ranar Laraba.
Ya kuma ce yana da Kwarewa da cancantar zama shugaban kasa a Najeriya.
Obi ya kuma bayar da tabbacin cewa, duka ‘yan Najeriya dake son Najeriya da arziki zasu taru ne dan kayar da Gwamnati me ci.