
Hukumar sojojin Najeriya ta gargadi kananan sojoji cewa, ba sai sun sha kwaya ba zasu iya aiki yanda ya kamata.
Kwamandan rundunar sojojin Najeriya ta 17 dake jihar Katsina, B.O. Omopariola ne ya bayyana haka a yayin wani tron karawa juna sani da aka gudanarwa sojojin kan matsalar tsaro.
Jami’an hukumar yaki da safarar miyagun Kwàyòyì NDLEA sun halarci taron inda suka wayarwa da sojojin kai game da hadarin ta’ammuli da miyagun kwayoyin.
B.O. Omopariola ya bayyana cewa bai yadda sai soja ya sha kwaya sannan zai iya aiki ba, yace sun yaki ‘yan ta’dda sosai amma babu sojan da yayi amfani da kwaya a lokacin.
Yace dan haka kada wani ya kawo mai maganar sai an sha kwaya sannan za’a iya aiki.