Ba Za Mu Iya Shiru Mu Bar Makiya Su Lalata Zaman Lafiya A Jihar Kano Ba, Cewar Kwankwaso
…ya zama dole mu bi hanyar da ta dace wajen ganin jihar Kano ta samu kyawawan tsari na zaman lafiya
Daga Muhammad Kwairi Waziri
Ɗan takarar shugabancin kasa a jami’yar NNPP Dr. rabiu musa kwankwaso ya bayyana hakan ne a mahaifarsa ta Madobi yayin ƙaddamar wata hanya mai tsawon kilomita 82.
Yace “akwai wasu mutane ne da suke son suci zarafin mu da sunan siyasa wanda ba zamu lamunci hakan ba ko waye shi, dan haka kuma a shirye muke damu taka duk wanda yake da niyyar taka mu a siyasar jihar kano” inji kwankwaso.