
Kakakin majalisar dattijai, Godswill Akpabio ya bayyana cewa, ba zai yiyu a yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ba irin abinda akawa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ba.
Watau ‘yan Adawa ba zasu iya cin zabe ba a zaben shekarar 2027.
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kayar da goodluck Jonathan zabe a shekarar 2015 a yayin da Jonathan din ke neman sake cin zabe a karo na 2.
Akpabio ya bayyana hakane a wani Bidiyonsa dake ta yawo a kafafen watsa labarai inda yace yankin Niger Delta Shugaba Tinubu zasu yi a zaben 2027.
Akpabio ya ce ‘yan Adawar sun yiwa Jonathan irin wannan abu a shekarar 2015 amma hakan ba zai faru akan Tinubu ba.