
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya bayyana cewa ba zai yiyu mutum yace shi dan PDP ne kuma dan jam’iyyar hadaka ta ADC ne a saidai mutum ya zai daya.
Gwamnan ya bayyana rashin jin dadinsa da ‘yan jam’iyyar PDP dake hada kai da ‘yan ADC.
Yana maganane a wajan taron jam’iyyar ind yace ba zasu amince da rashin da’a ba dolene mutum ya zabi daya ko ADC ko PDP.
Gwamnan yace hadakar ADC ba akan daidai suke ba.