
Wani Kwamandan Sojojin Najeriya a Arewa maso gabas inda ake fama da karuwar hare-haren ‘yan Bindiga na Bòkò Hàràm ya bayyana cewa ba zasu kyale ba, sai sun dauki fansa.
A kalla sasanin sojoji 10 ne mayakan Bòkò Hàràm da ÌŚWÀP suka farmawa da hare-haren.
Shugaban hedikwatar tsaro ta kasa, Christopher Musa ya bayyanawa sojojin cewa aka kokarin kai musu sabbin makamai kuma za’a magance matsalar ta tsaro inda ya karfafa musu gwiwa yayin ziyarar da ya kaiwa sojojin Borno.