Lauya Kola Alapinni ya aikewa da ofishin kakakin majalisar dattijai, Godswill Akpabio cewa basu amince da saka shari’ar Musulunci cikin kudin tsarin mulkin Najeriya ba.
Yayi hakan ne bayan kudirin dokar da dan majalisa Aliyu Bappa Misau ya gabatar a gaban majalisar cewa ya kamata a saka shari’ar Musulunci a tsarin kasuwanci da kwangila da sauransu.
An yi muhawara sosai a farfajiyar majalisar kan lamarin inda hakan ya jawo cece-kuce.
Lauyan ya kawo misali da cewa a kwanakin baya an rika kisa da kama wasu da suke aikata abubuwan da suka sabawa shari’ar Musulunci a Arewa inda yace su a kudu ba zasu akince da hakan ba.