Monday, December 15
Shadow

Ba zamu yafe abinda aka mana a Zaria ba>>Inji Sheikh Ibrahim Zakzaky

Shekara goma kenan tun bayan kisan da jami’an sojin Najeriya suka yi wa mabiya mazhabar Shi’a a garin Zaria na jihar Kaduna.

A wancan lokaci an yi amanna ɗaruruwan mutane ne suka mutu, da dama kuma suka jikkata, bayan zargin rundunar soji cewa mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky sun tare musu hanya.

Lamarin ya haddasa suka daga kungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam na duniya, waɗanda suka zargi sojoji da amfani da ƙarfi fiye da kima.

Shugaban dandalin tattauna al’amura naƙkungiyar mabiya Shi’a ta IMN a Najeriya, Farfesa Abdullahi Danladi, ya ce duk da wucewar shekaru goma tun bayan faruwar wannan mummunan lamari, har yanzu ba za su taɓa yafe wa waɗanda suka aikata wannan mummunan aikin ba.

Karanta Wannan  Ko a Mafarki ban taba Tunin za'a janye min 'yansandan dake bani tsaro ba>>Sanata Ningi

A tattaunawarsa da BBC, Farfesan ya ce raɗadin abin da ya faru na ci gaba da sosa zuƙatan al’ummar Shi’a, musamman ganin cewa babu wani bangare na gwamnati da ya ɗauki matakin hukunta masu laifi.

Ya ce, “Shekara 10 kenan da kashe mutanenmu, kuma har yanzu babu wanda aka kama. Gwamnati ta yi shiru, kwamitin da aka kafa don bincike ma bai fito da wani sakamako ba, balle a hukunta masu laifi.”

Farfesa Danladi ya ce abin da ya faru ya wuce abin da za a yi gum a kai, domin an kashe mutane ba tare da an ga adalci ba.

“Ba yadda za a ce an taru an kashe mutane, amma babu wanda ya fuskanci hukunci. Dole ne a dauki mataki domin hukunta wadanda suka aikata wannan ta’asa,” in ji shi.

Karanta Wannan  Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya alƙawarta samar wa sojojin ƙasar kayan aiki domin fatattakar ayyukan ƴanbindiga a arewacin ƙasar.

Ya kara da cewa akwai bayanai da ke nuni da cewa ana kokarin dakile wannan batu daga fitowa fili.

A cewarsa, “Akwai bayanan da ke nuna cewa ana kokarin rufe maganar. Amma irin wannan shari’a tana iya daukar lokaci ko tsawon shekaru, amma wata rana gaskiya za ta bayyana, ko da kuwa ba mu da rai. Tarihi ba zai manta da wannan mummunan aiki ba.”

Farfesan ya ce tunawa da lamarin bayan shekaru goma na kara tabbatar da matsayin su na rashin yafiya da neman adalci”.

“Idan irin wannan lokaci ya zo — musamman yanzu da yake shekara 10 dole ne zuciya ta sosa. Za mu taru mu fadakar da juna, mu kuma jaddada cewa ba za mu taɓa yafe wa ba, kuma muna jiran ranar da za a mana adalci a wannan duniya,” in ji shi.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Wannan wane irin Bala'ine? Gfresh ya koka kan yanda mata kawayensa ke son hurewa matarsa kunne

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *