Babban Hafsan Sojin Ƙasa ya bai wa dakarunsa wa’adin wata guda su kawar da ‘yan bindiga a Kwara.

Shugaban rundunar sojin ƙasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya bai wa sojoji umarnin su kawar da ‘yan bindiga daga Jihar Kwara cikin wa’adin wata guda.
Oluyede ya bayar da wannan umarni ne yayin da yake jawabi ga dakarun da ke barikin Sobi a Ilorin, babban birnin jihar.
Ya umarce su da su kawar da ‘yan bindigar daga ƙananan hukumomi biyu, yana mai jaddada cewa yana so a kammala aikin cikin wata guda.
Shugaban sojojin ya ce Najeriya ba za ta iya yarda ‘yan bindiga su sake bazuwa zuwa wani yanki na ƙasar ba.
Ya ƙara da cewa, ba za a yarda a samu wani irin taɓarɓarewar tsaro irin na Boko Haram a ko’ina cikin ƙasar ba.
Oluyede ya ce, “Don haka, kuna nan kuma na san za ku iya tabbatar da cewa waɗannan mutane (‘yan bindiga) sun bar wancan wurin ,” in ji shi yana magana da sojojin.
“In har suna son shiga wata ƙasa, wannan ba matsalarmu ba ce, amma dole ne ku kore su daga dazukan nan don kada mu sake samun wani sabon salo na Boko Haram da zai dame mu a nan”