
Matar tsohon shugaban kasa, Hajiya A’isha Buhari ta bayyana cewa, an so a fitar da ita daga fadar shugaban kasa lokacin mijinta na mulki amma taki yadda.
Tace wani jami’in tsaro ya ce mata ya kamata ta koma Daura da zama saboda suna son yin wani bincike idan an kammala sai ta dawo.
Saidai tace amma taki amincewa da hakan.
A’isha Kuma a cikin Littafin tarihin Rayuwar Buhari da aka rubuta tace babbar matsalar mijin nata yasan bara gurbi a gwamnatinsa amma yaki ciresu daga mukaminsu.
Tace tana fatan Shugaba Tinubu ba zai tafka irin kuskuren da mijin nata a tafka ba.