Friday, December 5
Shadow

Babu Abinda matasan Najeriya suka iya sai Korafi da zagin Shuwagabanni>>Inji Sanata Ireti Kingibe

Sanata Ireti Kingibe ta koka da cewa, Babu abinda matasan Najeriya suka iya sai korafi da zagin shuwagabannin.

Tace idan aka yi abu wani lokacin sai matasan su ce zasu yi zanga-zanga amma basa iyawa.

Tace wannan kasa taku ce, baku da wata kamarta, dan haka ya kamata ku tashi tsaye ku gyarata.

Tace amma yawanci ko Talakawa sun je kusa da masu mulki, yawanci suna neman abinda zai amfanesu ba ba wanda zai amfani Al’umma ba.

Karanta Wannan  TIRƘASHI: Añ bankado Natasha na wasa da hankalin jama'a ne kawai game da zargin Akpabio?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *