
Shugaban wata kungiyar dakewa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu kamfe, TSG Dr. Umar Tanko Yakasai yace babu inda hadakar ‘yan Adawa su Atiku zata je.
Ya bayyana hakane a Abuja inda yace ba zasu yi nasara ba saboda membobin dake cikin jam’iyyar sun samu dama a baya amma basu gyara Najeriya ba.
Yace ‘yan Najeriya ba zasu amince da hadakar ‘yan Adawar ba saboda sune suka yi wadaka da kudin gyaran wutar Lantarki da suka kai Dala Biliyan 16 da sauran wadaka da aka yi da kudin ‘yan Najeriya.
Yace shi kuma shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya zo ya gyara barnar da PDP ta yi ne.