
Babu Inda Na Ce Sai Mun Bada Cin Hancin Milyan Uku Kafin A Ba Mu Damar Gabatar Da Kudiri A Majalisar Tarayya, Cewar Hon Usman Ibrahim Auyo
Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Hadejia, Auyo da Kafin Hausa dake jihar Jigawa, Honarabul Usman Ibrahim Auyo, wanda ake yi wa lakabi da Kamfani ya nesanta kansa da labarin karya da aka yada akansa, wanda aka ce ya ce ba a ba su damar gabatar da kudiri a majalisa har sai sun bada cin hancin naira milyan uku ko fiye da haka. Sannan kuma sai sun yi ta kamun kafa ga sauran ‘yan majalisun.
A cewarsa ba ya na nufin majalisa ake baiwa wannan kudin ba, a duk sanda mutum zai gabatar da kudiri, akwai wadanda daga waje aikin su shine ka ba su kwangilar rubuta maka kudiri ka biya su, kafin daga bisani ka nemi shawarwari daga wajen takwarorinka ‘yan majalisu sannan ka gabatar da shi.
Sannan ya kara da cewa ba sai da kuduri mutum zai yi wa mazabarsa aiki ba, domin ko zuwa yanzu ya yi ayyukan birjik na more rayuwa ga mazabarsa.
A yayin da yake yi wa manema labarai jawabi, Honarabul Kamfani Auyo ya bayyana cewa wasu gurbatattun gidajen jaridu ne aka yi amfani da su wajen wallafa hakan a shafinsu domin cimma wata bukata ta siyasa sakamakon yadda yake kokari wajen samar da ayyuka lungu da sako na yankunan da yake wakilta.
Wanda hakan ya sanya wadansu masu zawarcin kujerarsa suke bibiyarsa shaŕri don ganin sun durkusar da tauraronsa da kawar da hankalinsa akan ayyukan da yake na kyautatawa al’ummarsa.
Honarabul Auyo ya cigaba da cewa kofa a bude take ga kowane dan majalisa domin ya gabatar da kudiri kan wasu al’amura da suka jibanci yankin da yake wakilta, don haka batun cewa sai sun bada rashawa kafin a ba su damar gabatar da kudiri ba gaskiya bane.
“Don haka ina kira ga jama’a da su yi watsi da wannan labari domin hankali ma ba zai dauka ba, duba da cewa majalisar tarayya tushe ce ta samar da dokar kasa.
“Wannan labarin ya fito ne daga masu yi mana bita da kullin siyasa don ganin an kawar da hankulin mu wajen hidimtawa al’aummarmu da muke yi”, inji Honarabu Kamfani..
Dangane da tallafa wa matasa, Auyo ya ce kashi 80% na rabon sa ya tafi hannun matasa ne wanda suka hada da babura da motoci. Da kuma ababen more rayuwa da ya samarwa al’ummar yankunansa.
Ya kuma bayyana cewa ya kafa doka cewa duk wani gari ko ƙaramar hukuma dake da korafi su rubuta su kaiwa hadimansa, sannan su jira mataki. Wanda idan abu ne da za a iya magancewa nan take, sai a yi, idan kuma ya shafi kasafin kuɗi, sai a saka shi a shekara mai zuwa.
A ƙarshe, Honarabul Kamfani ya yi magana mai kama da gargaɗi ga abokan hamayyarsa, inda ya ce babu ja da baya a 2027, sai abin da Allah Ya kaddara.