
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa sabuwar dokar Haraji da zata fara aiki a shekarar 2026 ba ruwanta da anda mutum ya samu kudi, ko ta hanyar data kamata mutum ya samu ko bata hanyar dta kamata ba, dole ya biya Haraji.
Shugaban Kwamitin shugaban kasa kan tsare-tsaren kudi da Gyara, Taiwo Oyedele ne a bayyana haka a cocin RCCG a wata ziyara da ya kai.

Yace idan dai mutum zai sayar da wani abu ko zai aikata wani abu ya samu kudi, ba ruwan gwamnati da wane irin aiki ne mutum ya aikata, sai ya biya Haraji, kamar yanda kafar Peoplesgazette ta ruwaito.
Gwamnatin tarayya dai na kokarin ganin ta karbi haraji daga kowane fanni na samun kudi dan ta tayar da komadar tattalin arzikin Najeriya.