Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya caccaki shuwagabannin kasashen Africa inda yace basu da godiyar Allah.
Ya bayyana hakane yayin da yake tattauna ci gaban da aka samu a yankunan Africa.
Yace tun shekarar 2013 suka girke sojojinsu inda suke taimakawa wajan yaki da ta’addanci da kuma magance matsalar juyin mulki da aka rika samu a wasu kasashen African.
Yace ba dan taimakon da suka bayar ba da wasu kasashen African yanzu ba kasashe bane sun dade da arwatsewa.
Yace amma shuwagabannin African basa ganin irin kokarin da kasar Faransar take musu, sojojinsu na sadaukar da rayuwarsu, amma ba’a godewa.
Idan dai za’a iya tunawa, kasar Nijar ta kori sojojin faransa daga cikinta.