
Kasar Canada ta yi sabuwar doka cewa, duk wanda zai je can cirani sai yana da Akalla Naira Miliyan 17 a Asusun bankinsa.
Wannan na zuwane bayan da aka yi sabuwar dokar shiga kasr ta Canada inda aka canja tsarin shiga kasar da ‘yan Cirani suke wanda ake kira da Refugees and Citizenship Canada (IRCC).
An fitar da sabuwar dokar ne ranar July 7, 2025 inda suka ce dai mutun na da Dalar Canada, CAD $15,263 kwatankwacin Naira Miliyan 17 kenan kamin ya je kasarsu.
A baya dai Abinda iyali na mutane biyu watau mutum da matarsa zasu mallaka kamin zuwa kasar Canada, Kudin Canadar Dala CAD $14,690 ne ake bukata.
Dama Duk shekara, kasar ta Canada na canja wadannan dokokin.