Kungiyar Kwadago NLC ta bayyana cewa, bata yadda da karin kudin kiran waya na kamfanonin sadarwa ba da aka yi zuwa kaso 50 cikin 100.
Shugaban kungiyar ta NLC, Joe Ajaero ne ya bayyana haka ranar Laraba ga manema labarai inda yace hakan ya zo ne a lokacin da ake fama da tsadar rayuwa gashi kuma babu kudin sayen kayan masarufi.
Joe Ajaero yace amfani da kafafen sadarwa ya zamarwa ‘yan Najeriya dole ta yanda suke kashe akalla kaso 10 cikin 100 na kudin shigarsu akan harkar sadarwa.
Joe Ajaero yace kungiyar kwadago ta yi Allah wadai da wannan lamari inda yace basu amince dashi ba.