
Jigo a jam’iyyar NNPP, Injiniya Buba Galadima ya bayyana cewa, yayi wuri ace an fara hadakar ‘yan Adawa dan zaben shekarar 2027.
Galadima ya bayyana hakane a hirar da Jaridar Punchng suka yi dashi inda yace Zumudin El-Rufai yayi yawa, yace ko da yake ba dan siyasa ban shiyasa amma yasa ba inda zashi.
Yace kamata yayi a bari shugaba Tinubu ya nutsu mayar da hankali wajan yiwa ‘yan Najeriya aiki.
Yace shi a yanzu ba zai ce komai akan mulkin Tinubu ba sai ya cika shekara biyu cif yana mulki kamin su duba suka yayi kokari ko akasin haka.