
Dan takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023 a jam’iyyar Labour party, Peter Obi ya bayyana cewa, sam bai ji dadin Hukuncin daurin rai da rai da aka yankewa Nnamdy Khanu ba.
Ya bayyana cewa tin farko bai goyi bayan kama Nnamdi Kanu ba.
Yace irin abinda Nnamdi Kanu ya zo dashi zama ake yi a yo sulhu ba da karfi ake amfani ba.
Kotun tarayya dake Abuja dai ta yankewa Nnamdy Khanu hukuncin daurin rai da rai bayan samunsa da laifin ta’ddanci.
Rahotanni sun ce tuni aka kaishi gidan yarin dake jihar Sokoto.