Friday, December 5
Shadow

Ban taɓa zuwa wurin boka don neman sa’a ba>>Inji Gwamnan Jihar Anambra, Charles Soludo

Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo ya yi watsi da raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa ya tuntuɓi wani boka domin buƙatar sake zaɓarsa matsayin gwamnan jihar a wa’adi na biyu.

Ranar 8 ga watan Nuwamban shekarar da muke ciki ne hukumar zaɓen Najeriya ta saka domin gudanar da zaɓen gwamnan jihar.

A cinin ƴan kwanakin nan ne wani bidiyo ya karaɗe shafukan sada zumunta da ke iƙirrarin cewa gwamnan ya tuntuɓi wani boka domin neman ”sa’ar” sake zaɓarsa.

To sai dai cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan, Christian Aburime, ya fitar, gwamnan ya bayayna zargin a matsayin ”tsagwaron ƙarya”.

Sanarwar ta ce bidiyon da ake yaɗawar an ɗauke shi ne a lokacin wani taro da jami’an gwamnati suka yi da masu wallafa abubuwa a shafukan sada zumunta na jihar.

Karanta Wannan  DA DUMI-DUMI: Sojoji Sun Harbe Wani DPO Na 'Yan Sanda A Jihar Zamfara Har Lahira Kan Zargin Safarar Makamai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *