
Tsohon Ministan Sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ya bayyana cewa, ba za’a hada baki dashi a kayar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zabe ba a 2027.
Hadi Sirika yace baya cikin hadakar jam’iyyar ‘yan Adawa ta ADC kuma baya shirin shiga.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin din Channels TV
Da aka tambayeshi me ya kaishi fadar shugaban kasa, sai yace sun jene dan yiwa shugaban kasar ta’aziyyar rasuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Yace me magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya tambayeshi wai ya ji ance ya shiga jam’iyyar ADC ta hadakar ‘yan Adawa inda yace masa ba gaskiya bane.